Watakila Juanma Lillo ya zama mataimakin Guardiola

Juanma Lillo

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Watakila Juanma Lillo ya kama aikin mataimakin Guardiola a Manchester United, bayan da ya bar aikin horar da Qingdao Huanghai ta China.

Dan kasar Spaniya ya yi nasarar kai Qindao babbar gasar China a kakar bara, amma yanzu wasu rahotanni na cewar zai yi aikin mataimakin koci a gasar Premier League.

Kamar yadda Daily Mail da Daily Mirror suka wallafa kocin yana da kwarewar da zai daga martabar Manchester City a wasannin kwallon kafa.

Guardiola bai da mataimaki tun bayan da Mikel Arteta ya karbi aikin jan ragamar Arsenal a cikin watan Disamba.

Wasu da aka sa ran za su maye gurbin Arteta a Etihad sun hada da Xabi Alonso da Vincent Kompany da sauran fitattun masu horar da tamaula.

Lillo ya tabbatar da barin kungiyar ta China wadda ya bai wa dalilin cewar zai je ya kula da mahaifiyarsa wadda ke fama da jinya.

Guardiola ya taka kwallo a karkashin Lillo a kungiyar Dorados ta Mexico daga nan ya yi ritaya daga taka-leda.

Lillo ya horar da Tolosa CF da Mirandes da Cultural Leonesa da UD Salamanca da Real Oviedo da Tenerife da Real Zaragoza da Ciudad Murcia.

Sauran kungiyoyin da ya ja ragama sun hada da Terrassa da Dorados da Real Sociedad da Almeria da Millonarios da Atletico Nacional da kuma Vissel Kobe.

Ya kuma yi aikin mataimaki a tawagar kwallon kafar Chile da kuma Sevilla mai buga gasar La Liga ta Spaniya.

Ranar 17 ga watan Juni za a ci gaba da gasar Premier, inda Manchester City za ta buga kwanatan wasa da Arsenal.

A kuma ranar za a kece raini tsakanin Aston Villa da Sheffield United.

Manchester City tana mataki na biyu a teburin Premier da tazarar maki 25 tsakaninta da Liverpool ta daya tun bayan da aka dakatar da wasanni a cikin watan Maruis saboda bullar cutar korona.

More News

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...

An yi zanga-zanga a fadar shugaban ƙasa da majalisar ƙasa kan dawo da Sarki Sanusi

Wasu masu zanga-zanga sun yi jerin gwano ya zuwa ƙofar fadar shugaban ƙasa da kuma majalisar dokokin ta tarayya kan dawo da Sarki Muhammadu...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ya kuma sanar da sake naɗa, Muhammad Sanusi a matsayin...

Sanusi ya sake zama Sarkin Kano

Shekaru hudu bayan sauke Muhammadu Sanusi II daga matsayin Sarkin Kano, Gwamna Abba Yusuf, na jihar Kano ya mayar da shi kan karagar mulki.Gwamnan...