Wata mata ta cinna wa gidan mijinta wuta saboda ya ƙi ya sake ta

Hukumomi sun kama wata amarya ‘yar shekara 20 mai suna Amina Hassan daga karamar hukumar Mubi ta Arewa a jihar Adamawa bisa laifin cinna wa gidan mijinta wuta.

Amina ta ɗauki wannan matakin ne saboda kin rubuta mata takardar saki.

An ce ma’auratan sun kulla yarjejeniya kafin aurensu.

A cewar wasu rahotanni, Amina ta sanar da iyayenta cewa ba ta da sha’awar yin wannan auren kwanaki kadan kafin ɗaurin auren.

Duk da haka, iyayenta sun dage cewa dole ne a yi bikin aure saboda sun riga sun raba katunan gayyata.

Bayan an daura auren ne ta nemi taimakon wani boka don ya sa mijinta ya tsane ta ya sake ta.

More from this stream

Recomended