Hukumar Alhazan jihar Niger ta ce karin daƴa daga cikin mahajjatan jihar ta riga mu gidan gaskiya a ƙasar Saudiyya.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, sakataren hukumar alhazan,Muhammad Aliyu ya ce mahajjaciyar ta mutu ne ranar Asabar da misalin ƙarfe 11 na safe.
Marigayiyar da aka bayyana da suna, Adeshetu Abubakar ta garzaya ta fito daga ɗakinta lokacin da jini ya riƙa fitowa ta hancinta da ta baki.
Aliyu ya ce mahajjaciyar daga ƙaramar hukumar Bida ta mutu ne sakamakon tsananin zafi bayan da ta dawo daga masallaci.
“Hajiya Adeshetu Abubakar mai shekaru kusan 65 ta fito daga ƙaramar hukumar Bida ta jihar Niger ta mutu ƴan sa’o’i kaɗan bayan da ta dawo daga masallacin harami,” ya ce.