Wasu Yara 6 Sun Yiwa Wata Matashiya Fyaɗe

Gwamnatin jihar Anambra ta samu nasarar ceto wata matashiya mai shekaru 19 da wasu da ake zargin wasu matasa da yara su 6 sun yi mata fyade a Anam dake karamar hukumar Anambra West ta jihar.

Misis Ify Obinabo, Kwamishiniyar Mata da Walwalar Jama’a ta jihar ta fadawa yan jarida ranar Asabar cewa an kama mutanen da suka aikata laifin.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Afam Ezenwa, shekara 17, Chijioke Ifeanyi, shekara 20, Collins Obadom,shekera 18, Abuchi Okechukwu, shekara 16, Chima Obiekezie, da Sunday Okafor, masu shekaru 27.

Obinabo ta ce tuni aka mika batun ga sashen aikata manyan laifuka na rundunar yan sandan jihar domin cigaba da bincike.

Ta ce ” lokacin da muka ga fefan bidiyon yarinya yar shekara 19 da ake zargin yara 6 sun yi mata fyade a Anam na yawo intanet mun yanke shawarar shiga cika lamarin tare da bibiyar halin da ake ciki.”

“An ceto wacce aka yi wa fyaden da haɗin gwiwar jami’an yan sanda suma waɗanda suka aikata an kama su. Ma’aikatar za ta tabbatar sun fuskanci hukunci.”

More from this stream

Recomended