
An sake shigar da wata kara a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja inda ake neman a cire Bola Ahmad Tinubu daga jerin masu takarar shugaban kasa a jam’iyar APC.
Umar Iliyasu,Suleiman Baba da Abubakar Adamu su ne suka shigar da karar a madadin kungiyar Gaskiya Youth Movement.
Masu ƙarar na neman a hana jam’iyar APC ta tsayar da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Takaradar karar ta bayyana cewa duba da shakku kan takardar karatu da kuma shekarun mutumin da suke kara bai kamata wanda ake kara na biyu wato jam’iyar APC ta kyale mutumin da ake kara na biyu Bola Tinubu ya tsaya takarar zaben fidda gwani ba na zaben shugaban kasa.
Har ila yau masu karar na son a hana Tinubu yin takara a karkashin kowace jam’iya a Najeriya.