Wasika daga Afirka: Abin da ya sa kare kai ba zai zama mafita ga satar mutane a Najeriya ba

Supporters of the

A jerin wasiÆ™unmu na Afrika, Æ´ar jaridar Najeriya kuma marubuciya Æ´ar Najeriya Adaobi Tricia Nwaubani ta yi duba a kan kira na baya bayan nan ga al’ummar Najeriya don kare kansu daga masu satar mutane.

Da alama gwamnatin Najeriya ta ba da shawarar cewa ba za a sake dogaro da ita ba don kiyaye lafiyar ‘yan kasa.

A makon da ya gabata, ministan tsaro ya aike da sako ga al’ummomin da suke fama da hare-hare daga kungiyoyin masu dauke da makamai, inda ya ce “ku kare kanku, ba kawai ku zauna a yi ta yanka ku kamar kaji ba.

“Bai kamata mu zama matsorata ba,” in ji Bashir Salihi Magashi, Manjo Janar mai ritaya.

“Ban san dalilin da ya sa mutane ke guduwa daga kananan abubuwa, kamar haka ba. Ya kamata su tsaya, wadannan mutane su sani cewa hatta mazauna kauyuka suna da kwarewa da kuma karfin da za su iya kare kansu,” in ji shi.

Maganar ta Magashi ta zo ‘yan sa’o’i bayan da wasu’ yan bindiga suka sace mutane da dama, ciki har da dalibai, daga wata makaranta a jihar Neja, da ke arewa ta tsakiya, abin da ya janyo martani daga yan Najeriya.

Mun riga mun saba da kula da lamuranmu a wuraren da gwamnati ba ta sauke nauyin da ke kanta ba.

Mutane da yawa a cikin kasar suna samar da tasu wutar lantarki, suna samarwa kansu ruwa, da kuma samar da ilimi ga yaransu da sauransu.

Adaobi Tricia NwaubaniAdaobi Tricia Nwaubani

No matter how determined an individual might be, they cannot defend themselves with just bare hands and bravery.”

Amma dokokin Najeriya ba su bayar da damar kowa ya sayi bindiga ba.

Komai irin azamar da mutane suke da ita, ba za su iya kare kansu da hannu kawai da kuma jaruntaka ba.

Mallakar makami a Najeriya ya kasance mai sarkakiya, da kuma wahalar gaske.

Ya danganta da nau’ikan bindigan, ya zama dole ka nemi izinin karamar hukumarka, ko ‘yan sandan jiharka, ko fadar shugaban kasa don samun lasisin da ya kamata a sabunta kowace shekara.

An dakatar da sabbin lasisin mallakar bindiga

Ana mika bukatar ne akalla cikin watanni shida, sannan akwai gwajin kwakwalwa da ake yi kafin a amince.

Duk wani mai bindiga da ke shirin yin tafiya ya kamata ya ba da makaminsa ga rumbun ajiya na ‘yan sanda don adana shi.

Kuma bayan mutuwar mai shi, za a mayar da makamin zuwa ga mahukunta.

Amma, shekaru biyu da suka gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan umarnin zartarwa inda kwata-kwata ya hana bayar da lasisin mallakar bindiga, matakin da aka yi imanin cewa martani ne ga karuwar rashin tsaro a kasar da kuma tsoron zubar da jini ba bisa ka’ida ba.

Kungiyoyin masu dauke da makamai, wadanda jami’an gwamnati da kafafen yada labarai na kasar suka fi sani da “‘yan fashi”, suna ta addabar arewa maso yammacin Najeriya da fashi da sace mutane.

An sace ‘yan siyasa,’ yan kasuwa, matafiya, da ‘yan makaranta a lokuta daban-daban, kuma galibi ana sakinsu bayan an biya kudin fansa.

Sauran yankuna na fuskantar dumbin matsalolin tsaro da suka hada da: mayakan Boko Haram, da rikicin manoma da makiyaya, da satar mutane, da satar fasaha da fashi da makami.

Kafafen yada labarai na cikin gida a wasu lokuta suna bayar da rahoton kokarin da kungiyoyin ‘yan banga suke yi na kiyaye muhallansu, galibi dauke da adduna da sanduna.

Amma wadannan makaman ba su dace da karfin wadanda suke kai harin ba, wadanda a fili doka da lasisi ba sa hana su mallakar makamai ta haramtacciyar hanya kamar AK-47 da sauran bindigogi.

“Wannan umarnin na zartarwa ya shafi bindigogin doka ne kawai kuma babu wanda zai magance wadanda suke da muggan bindigogi,” in ji tsohuwar ‘yar majalisa Nnenna Elendu-Ukeje a shekarar 2019, yayin wata muhawara da majalisar ta yi game da umarnin zartarwa na Shugaba Buhari.

Kamar yadda aka saba, talakawan ƙasar ne suka fi fama da rashin tsaro.

Bayanan hoto,
Daruruwan daliban da aka sace a Kankara a watan Disamba sun koma gida

Manyan ma’aikatan gwamnati a Najeriya galibi ana ba su ‘yan sanda masu dauke da makamai ta hanyar ofishinsu.

‘Yan Najeriya masu hannu da shuni galibi suna É—aukar’ yan sanda masu rakiya, har ma zuwa ayyukan sirri.

Wani babban jami’in dan sanda da ya zabi a sakaya sunan sa ya fada min cewa wasu masu fada a ji a wasu lokuta ma suna keta umarnin Mista Buhari ta hanyar sayen bindigogi sannan kuma su ba mutane cin hancin don su samu rasit da lasisi a baya.

Yawan makamai ba shi ne maslaha ba

To koma yaya ne dai, damuwar da akeyi a Najeriya game da haÉ—arin samun damar mallakar bindigogi a saukake abin dubawa ne, domin ana la’akari da halin da ake ciki a Amurka, inda ake yawan kashe kashe, sakamakon harbin bindiga.

To sai dai duk da tsauraran dokokin mallakar bindiga, har yanzu Najeriya na fama da yawaitar matsalolin tsaro.

Za ka sha mamakin irin jinin da za a zubar idan aka ce kowa ya soke bindiga a bayan rigarsa ya yi ta yawonsa a gari, don haka zai daya kawai shine jami’an tsaron Najeriya su tashi tsaye don sauke nauyin da ke kansu, na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ko da kuwa hakan na nufin kara yawan jami’ai.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miÆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaÆ™i da yiwa tattalin arzikin Æ™asa ne ya hana shi bayyana...

Ƴan sanda sun kama mutane biyu dake samarwa ƴan fashin daji makamai a jihar Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce tana tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da safarar bindiga a jihar. A wata sanarwa ranar...