Wani lamari mai matukar tayar da hankali da ban tausayi ya faru yayin da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wani matashi dan shekara 28 mai suna Misbahu Salisu bisa zarginsa da sanya wa jaririyarsa guba.
An bayyana cewa, wannan mummunan lamari ya faru ne saboda fifikon da mutumin ya yi wa ɗa namiji.
Lamarin ya faru ne a garin Doka Baici da ke karamar hukumar Tofa, lamarin da ya jefa al’umma cikin fargaba.
A cewar wata sanarwa da mataimakin babban kwamandan ayyuka na hukumar Hisbah ta jihar Kano, Mujahid Aminudeen, ya fitar, wanda ake zargin ya amince da aikata wannan mummunan aiki.
Bugu da kari, ya ba wa mahaifiyar jaririyar mai suna Sa’ade miyagun kwayoyi da wani kofin shayi da aka sa maganin barci kafin ya aikata laifin.
An bayyana wadannan bayanai masu ban tsoro yayin binciken hukumar.