Gwamnatin Jihar Borno, da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta kaddamar da wata katafariyar Ruga domin makiyayan jihar, a wani yunkuri na inganta harkar kiwo da kawo karshen rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin.
Wannan shiri na samar da Ruga ya samo asali tun zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, inda aka yi niyyar aiwatar da shi a jihohin Najeriya baki ɗaya. Sai dai, shirin ya gamu da turjiya a wasu jihohi.
Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), Alhaji Baba Usman Ngelzarma, ya halarci bikin kaddamar da Rugar da aka yi a ranar Asabar, 11 ga Janairu, 2025, a ƙauyen Garam-Nam da ke Ƙaramar Hukumar Mafa, Jihar Borno.
Alhaji Baba Usman ya bayyana cewa Rugar tana da nisan kilomita 10, kuma an samar da muhimman gine-gine ciki har da wuraren zaman makiyaya, filayen kiwo, gonakin noman ciyawa ga dabbobi, wuraren shan ruwa, da asibitocin kula da dabbobi.
Haka kuma, an gina wuraren koyar da makiyaya dabarun kiwo na zamani, sarrafa madara, da sauran abubuwan da suka dace domin inganta rayuwar makiyayan.
Gwamnatin Borno Ta Kaddamar Da Katafariyar Ruga Don Bunkasa Harkar Kiwo
