Wani riƙaƙƙen mai laifi da ya tsere daga gidan yarin Jos ya sake faɗawa hannun jami’an tsaro

Sojojin shiya ta ɗaya na rundunar haɗin gwiwa ta Operation UDO KA II dake yakin kudu maso gabas tare da haɗin gwiwar jami’an hukumar tsaro ta DSS na jihar Enugu sun kai wani samame maboyar yan ta’addar IPOB a jihar

Maboyar na kauyen Ugbakwa dake karamar hukumar Nkanu East ta jihar Enugu.

A yayin farmaki jami’an sun samu nasarar kama, Chimezie Chukwu wanda aka fi sani da Biggi da ya tsere daga gidan yarin Jos.

Biggi ya kasance fitaccen mai safarar bindigogi, kwayoyi baya da ficen da yayi a fashi da makami.

Kayan da aka samu a wurinsa sun haɗa da wayoyin hannu guda 6, baturan waya uku, na’urar POS ta Moniepoint, katin ATM, fakiti biyu da ake zargin tabar wiwi ce.

Naira dubu ɗari bakwai da ɗari biyu da tamanin aka samu a wurinsa.

A yanzu haka yana hannun jami’an hukumar tsaro ta DSS domin cigaba da bincike.

More from this stream

Recomended