Wani jirgin sama ya zarce cikin daji a filin jirgin saman Ibadan

Wani karamin jirgin sama mai ɗauke da rijistar namba N580KR ya sauka daga kan titinsa inda ya shige cikin daji a filin jirgin saman Ladoke Akintola dake Ibadan babban birnin jihar Oyo a ranar Juma’a.

Rahotanni sun nuna cewa jirgin na ɗauke da wasu muhimman mutane su 10.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, Carol Adekotujo mai magana da yawun hukumar FAAN dake lura da filayen jiragen saman Najeriya ta ce lamarin ya faru wajen karfe 11:00 na safe.

Adekotujo ta ce jirgin ya taso ne daga Abuja kuma ya sauka lafiya amma kuma ya gaza yin birki akan titinsa inda ya zarce cikin daji.

Lamarin na zuwa ne yan watanni kaɗan bayan wani jirgi dake ɗauke ministan wutar lantarki ya kusa ya yi hatsari a filin jirgin saman na Ibadan.

More from this stream

Recomended