Wani jami’in hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC ya gamu da ajalinsa bayan da wani direba ya matse shi a tsakanin motoci.
Shedun gani sun ce an matse jami’in na FRSC ne a tsakanin motoci inda kansa ya fashe ya yi ta zubar da jini.
Bisi Kazeem mai magana da yawun hukumar FRSC ya ce lamarin ya faru ne a yankin Orile-Iganmu a jihar Lagos ranar Asabar.
Sai dai Kazeem ga gaza bayyana ko an ankama direban motar da ya aikata haka.