Wani dan takarar gwamna ne zai tarbi Buhari a Zamfara?

Buhari

Za a kara samun rabuwar kawuna tsakanin ‘yan jam’iyyar APC yayin da Shugaba Buhari zai tafi Zamfara Yakin neman zaben Buhari a Zamfara.

A ranar Lahadi ne ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Zamfara a ci gaba da yakin neman zabensa na shugaban kasa a sassan jihohin Najeriya. Sai dai har yanzu jam’iyar APC ba ta san makomar ‘yan takararta na gwamna da yan majalisar tarayya da na jiha ba.

Idan har Buhari ya tafi Zamfara ba a san dan takarar gwamnan da zai tarbe shi ba, yayin da yan takara bakwai cikinsu har da ministansa na tsaro ke hamayya da dan takarar gwamnatin Abdulaziz Yari.

Bangaren Sanata Marafa da ke rikici da bangaren gwamna Abdulaziz Yari ya yi kira ga shugaba Buhari ya soke zuwa yakin neman zabensa a Zamfara.A wata hira da BBC, Sanata Marafa daya daga cikin masu neman takarar gwamna ya ce ba za su iya cudanya da bangaren gwamnati ba domin tarbo Buhari da kuma wajen yakin neman zabensa.

An dai kara shiga rudani game da rikicin APC a zamfara bayan hukuncin da kotuna biyu suka zartar a rana daya da ya ci karo da juna.Hukuncin wata babbar kotun tarayya a Abuja, ya tabbatar da matsayin hukumar zaben kasar na haramta wa duk ‘yan takarar jam’iyyar APC daga Zamfara shiga zabukan kasar da za a yi cikin watan gobe da na jibi.Hukuncin ya yi karo da na wata babbar kotun jihar karkashin mai shari’ah Muhammad Bello Shinkafi, da ta tabbatar da hukuncin cewa jam’iyyar APC reshen Zamfara ta gudanar da zabukan fitar da gwani, tare da ba hukumar zabe umurnin karbar ‘yan takararta don shiga zabukan kasar.

Sai dai mai shari’a Ijeoma Ojukwu ta kotun tarayya ta jaddada matsayin INEC inda ta ce jam’iyyun siyasa za su ci gaba da yin karan-tsaye ga ka’idojin zabe muddin suka kasa mutunta sharuddan da aka shata na jadawalin zabe.

Kotun ta ce hukuncin darasi ne ga sauran jami’yyun siyasa a nan gaba. APC a Zamfara ta gaza gudanar da dukkanin zaben fitar da ‘yan takararta na gwamna da na yan majalisar tarayya da na jiha.

Ana ganin kuma zuwan Buhari ba zai yi armashi ba saboda rikicn na APC a Zamfara inda aka samu rabuwar kai tsakanin bangaren gwamnati da ‘yan takara takwas da suka hada da mataimakin gwamna da ministan tsaro da kuma Sanata Marafa.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...