Wa Real ya kamata ta dauka tsakanin Pogba da Neymar?

Neymar Pogba

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Ranar Asabar Real Madrid ta karbi bakuncin Real Valladolid a wasan mako na biyu na cin kofin La Liga da suka kara a Santiago Bernabeu.

A karawar sun tashi ne 1-1, kuma Real ce ta fara cin kwallo ta hannun Karim Benzema saura minti takwas a tashi daga fafatawar.

Sai dai kuma ya rage saura minti biyu a kammala wasan ne Real Valladolid ta farke ta hannun Sergi Guardiola.

Wasu sakamakon wasannin mako na biyu a gasar La Liga:

Juma’a 23 Agusta 2019

  • Granada 0 – 1 Sevilla
  • Levante 2 – 1 Villarreal

Asabar 24 Agustan 2019

  • Osasuna 0 – 0 SD Eibar
  • Real Madrid 1 – 1 Real Valladolid
  • Celta de Vigo 1 – 0 Valencia C
  • Getafe 1 – 1 Athletic de Bilbao

Benzema ya yi iya kokarinsa a wasan na ranar Asabar, bayan kwallon da ya ci, karo da dama ya yi ta saukowa domin taimaka wa masu tsaron baya, domin su tsira da maki uku.

A gumurzun babu wani da ake sa ran zai zura kwallo bayan Benzema da ya wuce Luka Jovic, to amma bai taka rawar da ta dace ba, hakan ya sa magoya bayan Real ke ta kiran sunan Pogba.

Dan wasan Brazil, Neymar zai iya yanka tun daga tsakiyar fili ko daga gefe, zai kuma iya cin kwallo da ya samu dama, sai dai kuma rauni da yake fama da shi zai iya kawo masa cikas a wasu lokutan.

Neymar da Eden Hazard za su taka rawar gani a wasannin Real Madrid, ko da idan Hazard bai samu damar buga wasa ba, Neymar zai iya yin abin da ya dace domin kungiyar ta yi nasara.

A filin wasa na Santiago Bernabeu an ci gaba da kiran sunan dan wasan tawagar Brazil, Neymar domin ya koma saka rigar Real a bana.

Ranar 2 ga watan Satumba za a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon kafa ta Turai da ya hada da La Liga da Bundesliga da Serie A da Ligue 1.

A gasar ta La Liga da Madrid ta yi 1-1 da Valladolid, koci Zidane ya fara da ‘yan wasa James Rodriguez da Gareth Bale da kuma Isco, amma hakan bai sa sun hada maki ukun da ya kamata ba.

Sai dai abin tambaya wane dan kwallo ne Real take da bukata ne tsakanin Pogba da Neymar?

More News

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...