United ta sha dakyar a hannun FC Astana

Mason Greenwood (number 26) is the first player born in the 2000s to score a senior goal for Manchester United

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mason Greenwood (mai lamba 26) shi ne dan wasa na farko da aka haifa a shekarar 2000 da ya ci wa United kwallo

Dan wasan Manchester United Mason Greenwood, dan shekara 17, ne ya zura wa FC Astana kwallo daya tilo a raga a filin wasa na Old Trafford a Gasar Europa.

Greenwood mai sanya riga mai dauke da lamba 26, ya jefa kwallon ne a minti na 73 kuma wannan ne wasan na farko a babbar kungiyar United.

Sai dai hatta bayan da United ta ci wannan kwallon, ‘yan wasanta sun ci gaba da barar da damarmakin da suka samu.

A dayan wasan rukunin L, Partizan Belgrade ta yi 2-2 da AZ Alkmaar.

A ranar Lahadi ne United za ta kara da West Ham a Gasar Premier yayin wasanta na gaba da kungiyar AZ Alkmaar ranar 3 ga watan Oktoba.

More from this stream

Recomended