UAE Golden Visa: Yadda za ku iya samun bizar shekara goma ta zama a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Digirin Digirgir

Immigration control for Dubai international airport

Tun bayan da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta sanar da shirinta na bayar da bizar shekara 10 ga masu digirin digirgir zuwa kasar mutane suke ta neman yadda wanna tsari yake.

Mataimakin shugaban ƙasar kuma firaiministan ƙasar Sheikh Mohammed ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter yana cewa za su bayar da bizar ne ga waɗanda suka kammala jami’o’in kasar da sakamakon karshe da ya kai maki (GPA) 3.8 zuwa sama.

Sauran kwararru a wasu fannonin ilimi kamar masana kimiyyar haɗa makamashi da ke ƙasar suma za su iya samun wannan biza.

Ga jerin rabe-raben mutanen da za su iya samun bizar zama a UAE ta shekara 10

Idan injiniya ne kai a ɓangare;

  • Computer science,
  • Electronics
  • Programming,
  • Electricity
  • Biotechnology

Idan kwararre ne kai a bangaren;

  • Artificial Intelligence
  • Big data
  • Virology
  • Epidemiology

Haka zalika idan ka gama makaranta a ƙasar da sakamako mai kyau, kai da iyalanka za ku samu wannan biza ta shekara 10.

Alfanun da ke cikin wannan biza

Mutum zai samu damar zama a ƙasar na tsawon shekara 10, kuma idan ta ƙare za a iya sabunta ta.

Za ta bai wa mutum damar zama ya yi aiki ko kuma kasuwanci cikin tsawon waɗannan shekaru.

Masu irin wannan bizar na da damar yin tafiya ciki jihohin UAE ba tare da wani shamaki ba.

Bizar za ta bai wa waɗanda suke zaune su kaɗai damar gayyatar iyalansu su ziyarce su, suma kuma su shiga tasa inuwar su samu tasu bizar.

Yadda za ka iya yin karatu a UAE

Za ka iya neman duk makarantar da kake so ta intanet.

Idan kana son samun biza domin yin karatu a UAE, kana bukatar wani mazaunin kasar ya yi maka garanto.

Idan ba ka da wani wanda kake da laƙa da shi ko kuma wakusanci a ƙasar, to jami’ar da ta baka wannan gurbi za ta tsaya maka.

Nawa ne karatu a UAE

Kudin makaranta a ƙasar ya sha ban-ban, ya danganta da jami’ar da mutum ya samu, a inda take da kuma matakin karatunsa da abin da zai karanta.

Misali kamar birnin Dubai wanda ya fi tsadar rayuwa a ƙasar, kudin makaranta ga masu digirin farko ya kusa dalar Amurka 10,000 zuwa 20,000 a shekara ga kuma masu yin mastas kudin na farwa daga dalar Amurka 15,000 ne zuwa 20,000 a shekara.

Amma ba wai ko ina ne ke da irin wannan farashi ba a faɗin ƙasar.

Yadda za ka yi karatu a UAE kyauta

Za ka iya neman ko wacce jami’ar kasar da ke ba da tallafin karatu ta shafinsu ta intanet. Ka tabbatar ka samu makin da suke buƙata kuma ka cika dukkanin sharuɗansu kan ɗalibai ‘yan ƙasar waje da ke karatu a kasar.

Za kuma ka iya neman tallafin karatun da gwamnati ke bayarwa kyauta zuwa UAE idan ka cika sharudan hakan a ƙasarka.

Za ka iya neman tallafin karatu kyauta a wasu wuraren da ba na gwamnati ba, akwai kuma kamfanoni da suke bayar da wannan tallafi ga ɗalibai a UAE.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...