Tudun Biri:An gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya

Masu zanga-zanga a ranar Laraba sun tsinkayi ginin majalisar dokokin tarayya dake Abuja kan kisan da jirgin sojoji ya yiwa fararen hula a Kaduna ranar Lahadi.

Masu zanga-zangar wanda suka rufe kofar shiga majalisar har tsawon kusan awanni biyu sun bukaci a yi adalci ga waÉ—anda abun ya shafa sun kuma yi kira ga ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da ya mayar da hankali kan aikinsa ko kuma ya ajiye mukaminsa.

Sama da mutane 100 ne suka mutu a harin da wani jirgin sama marar matuki na rundunar sojan Najeriya ya kai a ƙauyen Tudun Biri dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Har ila yau sama da mutane 60 suka jikkata a harin da yanzu haka suke samu kulawa a asibitocin jihar daban-daban.

Da yake wa manema labarai jawabi, jagoran zanga-zangar a ƙarkashin kungiyoyin majalisar matasan Najeriya ta NYCN da kuma Arewa Youth Movement, Nasir Ishaku ya bukaci ayi adalci ga waɗanda avun6ya shafa.

Ya ce kisan Æ´an Najeriya a kullum musamman a yankin Arewa abu ne da baza a lamunta ba.

Ishaku ya shawarci majalisar da ta gudanar da binciken kisan na ranar Lahadi kana ta É—auki kwakkwaran mataki akai.

More News

Tinibu ya aikawa da majalisar dattawa sunaye 7 na  ministocin da zai naÉ—a

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga majalisar dattawa da ta tabbatar da sunayen mutane 7 da ya tura majalisar da zai...

Gwamnatin Abia za ta fara biyan albashi mafi maranci na naira 70,000 a watan Oktoba

Gwamnatin Jihar Abia ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon albashi mafi karanci na naira 70,000 ga ma’aikatanta daga watan Oktoba 2024.Kwamishinan...

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...