Tudun Biri:An gudanar da zanga-zanga a majalisar tarayya

Masu zanga-zanga a ranar Laraba sun tsinkayi ginin majalisar dokokin tarayya dake Abuja kan kisan da jirgin sojoji ya yiwa fararen hula a Kaduna ranar Lahadi.

Masu zanga-zangar wanda suka rufe kofar shiga majalisar har tsawon kusan awanni biyu sun bukaci a yi adalci ga waɗanda abun ya shafa sun kuma yi kira ga ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da ya mayar da hankali kan aikinsa ko kuma ya ajiye mukaminsa.

Sama da mutane 100 ne suka mutu a harin da wani jirgin sama marar matuki na rundunar sojan Najeriya ya kai a ƙauyen Tudun Biri dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Har ila yau sama da mutane 60 suka jikkata a harin da yanzu haka suke samu kulawa a asibitocin jihar daban-daban.

Da yake wa manema labarai jawabi, jagoran zanga-zangar a ƙarkashin kungiyoyin majalisar matasan Najeriya ta NYCN da kuma Arewa Youth Movement, Nasir Ishaku ya bukaci ayi adalci ga waɗanda avun6ya shafa.

Ya ce kisan ƴan Najeriya a kullum musamman a yankin Arewa abu ne da baza a lamunta ba.

Ishaku ya shawarci majalisar da ta gudanar da binciken kisan na ranar Lahadi kana ta ɗauki kwakkwaran mataki akai.

More from this stream

Recomended