Tottenham: Sissoko zai yi jinya zuwa watan Afirilu

Tottenham

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Dan wasan Tottenham, Moussa Sissoko zai yi jinya zuwa watan Afirilu, bayan aiki da likitoci suka yi masa a gwiwar kafarsa.

Dan kwallon mai shekara 30, ya yi raunin ne a wasan da Tottenham ta yi rashin nasara a hannun Southampton da ci 1-0 a sabuwar shekarar 2020.

Dan wasan tawagar Faransa ya buga wa Tottenham wasa 20 daga 21 da ta yi a Premier bana, inda ya ci kwallo biyu a raga.

Tottenham ta ce za ta sa ido kan jinyar da zai yi, domin ya koma fagen fama a farkon watan na Afirilu.

A makon jiya ne Tottenham ta sanar Harry Kane zai yi jinya, koda yake ba a fayyace lokacin da zai koma buga kwallo ba.

Tottenham tana ta shida a kan teburin Premier League, maki biyar tsakaninta da Chelsea ta hudu a teburin.

More from this stream

Recomended