Tiyatar da aka yi wa Gbamin ta yi kyau – Ancelotti

Jean-Philippe Gbamin
Dan wasan na Côte d’Ivoire ya buga wasanni biyu ne kacal ga kungiyar tasa a wannan kakar tun bayan sayen sa da ta yi a kan euro miliyan 25

Mai horas da Everton Carlo Ancelotti ya ce tiyatar da aka yi wa dan wasan tsakiyar kungiyar Jean-Philippe ta yi kyau, kuma yana ci gaba da murmurewa.

Ya ce ana sa ran zai iya dawowa murza leda nan da makwanni takwas masu zuwa.
Dan wasan na Côte d’Ivoire ya buga wasanni biyu ne kacal ga kungiyar tasa a wannan kakar tun bayan sayen sa da ta yi a kan euro miliyan 25.
Sai dai bayan yi masa tiyata ta biyu, Ancelotti ya ce tiyatar ta yi kyau kwarai kuma yana ci gaba da samun lafiya kawo yanzu.
A wani labarin kuma, an shirya wa Andre Gomes wani wasan sada zumunci yayin da yake shirin dawowa fage a wannan watan bayan doguwar jinyar da ya sha fama da ita, saboda rauni a gwiwarsa da ya samu.
Mai horarwar ya ce ana sa ran Gomes zai dawo buga wasa a karawar da Everton za ta yi da Arsenal a ranar 23 ga watan Fabrairu.
Kungiyar ta samu hutu bayan karawar da ta yi da Crystal Palace a ranar Asabar kafin su ziyarci Arsenal a nan gaba.
Da aka yi masa tambaya a kan ko yana da yakinin cewa dan wasan zai buga karawa da Asenal, sai ya kada baki ya ce ”muna fatan hakan”.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...