Tinubu zai sauya wa ministocinsa ma’aikatu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kammala shirye-shiryen kawo sauyi a majalisar ministocinsa nan ba da dadewa ba, wanda zai hada da nada sabbin ministoci da kuma kafa sabuwar ma’aikata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sabuwar ma’aikatar za ta kasance ne ta raya dabbobi, wanda ya zuwa yanzu a karkashin ma’aikatar noma da raya karkara take, da nufin tafiyar da tsarin kula da kiwon dabbobi na gwamnati.

Babban tsarin kula da dabbobin Najeriya da aka kaddamar a watan Agustan shekarar da ta gabata, an kafa shi ne domin jagorantar ci gaban fannin kiwon lafiya wanda ya kai kusan kashi daya bisa uku na gudummawar kashi 21 cikin 100 da bangaren noma ke bayarwa ga illahirin arzikin cikin gida na kasa (GDP).

More from this stream

Recomended