Tinubu ya ziyarci Oba na Lagos

0

Zaɓaɓɓen shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya ziyarci Oba na Lagos, Rilwan Akiolu a fadar sa dake Lagos.

Tinubu ya kai ziyarar ne domin yin godiya ga sarkin tare da nuna masa shedar da aka ba shi ta cin zaɓe.

A makon da ya gabata ne hukumar zabe ta INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban kasa da aka gudanar na ranar Asabar.