Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa birnin Paris na kasar Faransa da yammacin yau Talata.
Tawagar kafafen yada labaransa ce ta yada hoton bidiyon yadda Tinubu ke sauka daga jirgin shugaban kasa a shafin Twitter.
Shugaban ya je kasar Turai ne domin halartar taron bayar da kudade na duniya, wanda shugaba Emmanuel Macron ya kira.
Wannan dai ita ce ziyarar aiki ta farko da Tinubu zai fita daga Najeriya tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a ranar 29 ga Mayu, 2023.