Tinubu ya roĆ™i ma’aikatan lafiya da su janye yajin aiki

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, a ranar Litinin, ya gana da shugabannin kungiyar ma’aikatan lafiya, JOHESU.

Kungiyar ta kwashe sama da mako guda tana yajin aiki, inda ta janye mambobinta daga asibitocin gwamnati a fadin kasar.

A ganawar tasu ta ranar Litinin, Mista Tinubu ya bukaci kungiyar JOHESU da ta janye yajin aikin ta kuma baiwa mambobinta, ma’aikatan lafiya da likitoci hakuri da su koma bakin aiki.

Bayanin taron na kunshe ne a cikin sanarwar da Abiodun Oladunjoye, daraktan yada labarai na fadar gwamnatin jihar ya fitar.

“Bangaren lafiya bangare daya ne da ke da muhimmanci ga bil’adama. Za mu warware dukkan matsalolin,” in ji Mista Tinubu a wajen taron.

More News

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma’aikatar kudin jihar ta miĆ™ata bayanan bashin da El-Rufai ya ciwo

Majalisar dokokin jihar Kaduna ta nemi ma'aikatar kudi ta jihar da ta miƙa mata cikakken bayani kan basukan  da gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Nasiru...

An dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air

Festus Keyamo, ministan harkokin sufurin jiragen sama ya umarci hukumar FAAN dake lura da sufurin jiragen sama a Najeriya ta dakatar da ayyukan kamfanin...

Gwamantin Kano na kashe naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha—Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano na kashe kimanin naira biliyan 1.2 duk wata don samar da ruwan sha na tafi da gidanka a cikin babban birnin...

Yahaya Bello Ya Bayyana Dalilan Da Ya Hana Shi Bayyana A Gaban Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ce tsoron kamun  hukumar EFCC dake yaĆ™i da yiwa tattalin arzikin Ć™asa ne ya hana shi bayyana...