Tinubu ya miƙa tuta ga ƴan takarar APC a zaɓukan gwamna na jihohin Kogi, Bayelsa da Imo

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya miƙa tuta ga yan takarar gwamna a jam’iyar APC a zaɓen da za ayi a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo.

A ranar 11 ga watan Nuwamba ne aka shirya gudanar da zaɓukan gwamna a jihohin uku.

Ƴan takarar na jam’iyar APC sun haɗa da Hope Uzodimma wanda yake neman a sake zaɓensa a matsayin gwamnan jihar Imo, sai Timpre Sylva a jihar Bayelsa da kuma Usman Ododo wanda yake neman a zaɓe shi a matsayin gwamnan Kogi.

Tinubu ya yi kira da a gudanar da sahihin zaɓe ba tare da tahin hankali ba.

A yan kwanakin nan hukumar zaɓe mai zaman kanta ƙasa INEC ta nuna damuwarta kan yadda ake yawan samun rikice-rikice da ya shafi ƴan takara da kuma jam’iyunsu a jihohin uku

More from this stream

Recomended