Tinubu ya gana da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga Sarki Charles na Birtaniya a fadar Buckingham a wata ziyara da yakai.

Wannan ce ganawa ta farko da shugabannin biyu suka yi tun bayar wacce suka yi a birnin Dubai a wurin taro kan sauyin yanayi na COP 28 da aka yi a shekarar da ta wuce.

A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa , Bayo Onanuga Sarki Charles ne ya buƙaci ganawar.

Onanuga ya ce dukkanin shugabannin biyu sun tattauna kan abubuwan da suka yi tarayya akai ciki har da batun gaggauta mayar da hankali kan  sarkakiyar dake tattare da batun sauyin yanayi.

Tinubu da Sarki Charles  sun duba batun lalubo damarmaki dake buƙatar haɗa karfi da ƙarfe dan tunkarar taron COP 29 da za ayi a ƙasar  Azerbaijan da kuma taron kasashe rainon Ingila da za ayi a Samoa.

More from this stream

Recomended