Shugaba Bola Tinubu ya amince da dakatar da shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, AbdulRasheed Bawa daga aiki.
Ya yi haka ne domin ba da damar gudanar da bincike mai inganci a kan yadda yake gudanar da ayyukansa a lokacin da yake kan mulki.
A cewar sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar, matakin ya biyo bayan zarge-zargen “mai nauyi” na cin zarafin ofishin da aka yi masa.
“An umurci Mista Bawa da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Daraktan Ayyuka a Hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin Shugaban Hukumar har zuwa karshen binciken,” in ji sanarwar.