Tinubu Da Gwamnoni Na Cigaba Da Ƙoƙarin Cire Ƴan Najeriya Daga Talauci- Gwamna Yahaya

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma gwamnonin fadin kasarnan na cigaba da kokari matuka wajen fitar da yan Najeriya daga halin matsin tattalin arzikin da suke ciki.

Gwamnan ya kara da cewa cin alwashin da shugaban kasa Tinubu ya yi na samar da ingantaccen shugabanci zai taimaka wajen habaka yanayin tattalin arzikin da ake ciki nan bada jimawa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin kaddamar da rabon tallafin kayan abinci kashi na biyu a karamar hukumar Gombe da aka yi a fadar sarkin Gombe.

Ya bayyana cewa fadaɗa shirin da kuma cigaba da samar da tallafin anyi shi ne domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Ya ce shirin ana sa ran zai samar da tallafi ga mutane matalauta dubu casa’in.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani ɓangare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta ɗaure mutumin sa ya yi sama-da-faɗi da kuɗin marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...