
Taiwo Akinwumi mutumin da ya kirkiro da tutar Najeriya ya mutu.
Akinwumi Akinwumi ɗaya daga cikin ƴaƴansa shi ne ya sanar da mutuwar mahaifin nasa cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter a baya.
Kawo yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tarayya ko na jiha kan mutuwar.