Sojojin sun kashe yan bindiga 5 a Kaduna

Rundunar sojan Najeriya Shiya Ta Ɗaya sun kashe wasu yan bindiga 5 da suka jima suna addabar wasu al’ummomi dake jihar Kaduna.

Mai rikon muƙamin daraktan yada labarai na rundunar sojan Najeriya Shiya Ta Ɗaya, Musa Yahaya cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce an kashe yan bindigar ne a musayar wuta da suka yi ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce an yi musayar wutar ne a yayin kakkabe yan bindiga a Kanti-Tantatu a dajin Kabusu da tsaunin Kaso dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Bindigogi kirar AK-47 guda huɗu da baburan hawa uku na daga cikin abubuwan da aka samu a wurin yan bindiga.

More from this stream

Recomended