Sojojin Nato za su bar Afghanistan bayan kulla yarjejeniya

Soja dauke da bindiga

Hakkin mallakar hoto
Reuters

—BBC Hausa

Image caption

Akwai sauran dakarun Amurka guda 12,000 a Afghanistan inda aka shafe shekara 18 ana gwabza yaki

Wata sanarwar hadin gwiwar da gwamnatocin Amurka da Afghanistan suka fitar ta bayyana cewa dakarun Amurka da na kasashen rundunar tsaro ta Nato za su fice daga Afghanistan a cikin wata 14.

Sanarwar ta ce soojojin za su bar Afghanistan ne da zarar kungiyar Taliban ta cika sharuddan yarjejeniyar zaman lafiya da za a sanya wa hannu nan gaba.

A ranar Asabar 29 ga Fabrairu 2020 ne za a rattaba hannu a kan yarjejeniyar a kasar Qatar, da zummar kawo zaman lafiya a Afghanistan bayan shafe shekaru 18 ana gwabza yaki.

Baya sanya hannu a kan yarjejeniyar, gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban za su ci gaba da tattaunawa a kan sauran batutuwa.

Sanarwar da Amurka da Afghanistan suka fitar ta ce: “Kasashen kawance za su gama kwashe ragowar sojojinsu daga Afghanistan cikin wata 14, daga lokacin da aka kulla yarjejeniyar tsakanin Amurka da Taliban …bisa sharadin Taliban ta cika nata bangaren yarjejeniyar”.

A shekarar 2001 ne Amurka ta fara jibge dakarunta a Afghanistan bayan hare-haren ranar 11 ga watan Satumba da kungiyar al-Qa’eda ta kai a Amurka.

An kashe sojojin Amurka 2,400 tun bayan zuwansu Afghanistan, inda har yanzu akwai sauran dakarun Amurka guda 12,000.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin kawo karshen yakin na Afghanistan.

Yaya Taliban da Amurka suka fara tattauwana?

Tun a shekarar 2011, Qatar ke karbar bakuncin shugabannin Taliban da suka koma kasarta domin tattauna batun kawo zaman lafiya a Afghanistan.

Yunkurin ya yi ta samun tsaiko. A 2013 an bude ofishin Taliban, amma aka rufe shi saboda cacar baki game da sanya tutoci, lamarin da ya kawo cikas ga tattaunawar.

A watan Disamban 2018, Taliban ta sanar da cewa za ta gana da jami’an gwamnatin Amurka domin “lalubo hanyar zaman lafiya”.

Sai dai kungiyar ta sha kin amincewa ta tattauna da jami’an gwamnatin Afghanistan saboda zarginsu da zama “karnukan farautan” Amurka.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Cimma matsaya

Bayan tattauna sau tara tsakanin Taliban da Amurka a Qatar, da alama bangarorin sun kusa samun daidaito.

A watan Satumbar 2019, babban mai shiga tsakani na gwamnatin Amurka ya ce kasarsa za ta janye soja 5,400 daga Afghanistan cikin mako 20 a matsayin alkawarin fahimtar juna da suka yi wa Taliban.

Kwanaki kadan bayan nan, Shugaba Trump ya ce tattaunawar “ta rushe”, saboda mayakan Taliban sun kashe wani sojan Amuka. Amma cikin mako biyu, bangarorin suka ci gaba da tattauna a sirrance.

A makon da ya gabata Taliban ta amince da “rage kai hare-hare” – sai dai hukumomin Afghanistan sun ce mayakan kungiyar sun kashe soja 22 da fararen hula 14 a dan tsakanin.

Me ya haddasa yakin Afghanistan?

Yakin Afghanistan ya fara ne bayan Amurka ta fara kai hare-haren sama a kasar wata daya bayan harin ranar 11 ga watan Satumbar 2001 da aka kai Amurka.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Taliban a Afghanistan – a wannan lokacin – ta ki mika wa Amurkar mutumin da ake zargin ya shirya harin, wato Osama bin Laden.

Amurka ta samu goyon bayan kawayenta inda cikin dan lokaci suka kawar da mulkin gwamantin Taliban a Afghanistan.

Hakan ya sa Taliban ta zama ‘yar tayar da kayar baya, tare da kai munanan hare-haren da suka hana gwamnatocin da suka biyo baya sakat.

Aikin rundunar kawancen kasashen ta kammala aikinta a 2014, amma ta ci gaba da zama domin horas da sojojin Afghanistan.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...