Sojojin Afghanistan sun kwace iyaka da Pakistan

Dakarun gwamnatin Afghanistan sun kwace yankin iyakar kasar mai muhimmancin da kasar Pakistan daga hannun tsagerun kungiyar Taliban masu dauke da makamai. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito halaka mai daukan hoton kamfanin a yankin.

Mako guda da ya gabata ‘yan Taliban suka kwace yankin iyakar. Shaidun gani da ido daga bangaren Pakistan sun bayyana irin dauki ba dadin da aka tafka tsakainin bangaren biyu gabanin samun nasarar dakarun gwamnatin Afghansitan na sake kwace yankin mai tasiri.

Tun lokacin da aka bayyana kudirin janye dakarun kasashen duniya daga kasar ta Afghanistan bayan shafe kimanin shekaru 20, ‘yan Taliban suke amfani da damar wajen sake kwace yankuna da dama daga dakarun gwamnati.

More News

Ƴan Fashin Daji Sun Kashe Mutane 7 A Jihar Kebbi

Mutane 7 aka bada rahoton ƴan fashin daji sun kashe  a garin Tudun Bici dake ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi. A cewar mazauna...

Tsoffin gwamnoni sun wawashe sama da naira tiriliyan 2 tun komawa dimokuraÉ—iyya

Aƙalla tsoffin gwamnoni 58 ne ake zargin sun wawure kuma sun yi almubazzarancin jimillar naira Tiriliyan 2.187 a cikin shekaru 25 tun komawa mulkin...

Ƴan sanda sun kama mutane 50 kan rikicin da ya faru a wata kasuwa a Lagos

Rundunar Æ´an sandan jihar Legas ta kama mutane sama da 50 da ake zargin suna da hannu rikicin da ya faru a kasuwar Ile...

Ƴan Sanda sun kama wanda ya shirya kai harin jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a shekarar 2022

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce jami'anta sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Abdullahi wanda ake zargi da kitsa harin jirgin ƙasar da...