Sojoji sun kashe kwamandojin ƴan ta’adda a Najeriya

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta ce bangarenta na rundunar Operation Hadin Kai a ranar 10 ga watan Janairu ya kawar da wasu manyan kwamandojin ISWAP da ‘yan ta’adda uku a Borno.

Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaron, Maj.-Gen. Edward Baba, ne ya bayar da wannan tabbacin a cikin rahoton mako-mako na ayyukan rundunar a ranar Juma’a a Abuja.

Mista Buba ya ce kwamandojin uku an bayyana sunayensu kamar haka: Abou Maimuna, Abou Zahra da Kwamanda Saleh tare da kwamandansu a cikin kwalekwale.

Har yanzu dai jami’an tsaron Najeriya na ta fama ba dare ba rana wajen ganin sun kawar da ta’addanci a fadin ƙasar amma abin ya ci tura.

More News

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Mahaifi ya fille kan ɗiyarsa don yin asiri

Jami’an tsaro na jihar Edo sun kama wani mutum mai suna Emmanuel Ovwarueso bisa zarginsa da fille kan diyarsa bisa zarginta da laifin kashe...

Majalisar dokokin Zamfara ta tsige kakakinta saboda tsanantar rashin tsaro a jihar

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, tare da nada Bashar Gummi, a matsayin kakakin majalisar. Hakan ya biyo bayan kudirin da dan...

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane shida da wasu ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari a jihar. Jami’in hulda...