
Rundunar sojan Najeriya tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kama wasu mutane 5 da ake zargin su da kasancewa mambobin kungiyar Eastern Security Networ(ESN)
ESN bangare dake fada da makamai na kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra.
Mutanen dai sun fada hannun jami’an tsaro a ranar Litinin a dajin Orsomoghu da ya hada jihohin Imo da Anambra.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Talata mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Onyeama Okechukwu ya ce an kama mutanen ne a yayin wani samame da aka kai kan masu ta tabbatar da dokar hana fita ranar Litinin a yankin kudu maso gabas.
Sanarwar ta ce duk da cewa mutanen sun tayar da bama-bamai tare da bude wuta jaruman sojojin sun samu nasarar kama wasu a yayin da wasu suka tsere da raunin harbin bindiga.
A karshe sanarwar ta bayyana cewa sojoji biyar da yan sanda biyu ne suka samu raunuka sanadiyar fashewar bam a yayin farmakin.