Sojoji sun kama mai sayarwa da ƴan fashin daji miyagun kwayoyi a Kaduna

Dakarun soja sun samu nasarar kama wani mai shagon sayar da magani wanda yake sayar da miyagun kwayoyi ga ƴan fashin daji da kuma masu kai musu bayanai a ƙauyen Katari dake ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Wani shugaban al’umma dake yankin ne  ya faɗawa wakilin jaridar Daily Trust a yayin wata zantawa ta wayar tarho  a ranar Laraba cewa an kama mutumin ne a ranar Talata bayan da aka kama wasu mutane biyu a  Marabar Idda da ake zargin masu bawa ƴan fashi daji bayanai ne.

” Ya ce mutumin wanda ya mallaki wani shagon kemist ya amince cewa yana sayar da miyagun kwayoyi ga ƴan fashin daji da kuma masu kai musu bayanai,” ya ce.

Kawo yanzu rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba t fitar da wata sanarwa ba kan mutanen da aka kama.

More from this stream

Recomended