Sojoji sun ceto mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a Kaduna

Dakarun soja sun samu nasarar ce to wasu mutane uku daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro na jihar, Samuel Aruwan shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Aruwan ya ce an samu nasarar ce to mutanen ne tare da lalata maboyar yan bindigar a dazukan Chikun, Kachia da kuma Kajuru.

More from this stream

Recomended