
Sojojin rundunar Operation Desert Sanity 2 sun samu nasarar ceto biyu daga cikin ma’aikata uku na kungiyar agaji ta Family Health International (FHI360) da mayakan kungiyar ISWAP suka sace a Borno.
Mayakan na ISWAP sun sace ma’aikatan agajin ne tare da wasu jami’an tsaro biyu a wani hari da suka kai masaukin su dake Gamborun Ngala a ranar 26 ga watan Afrilu.
Wata majiya ta bayyana cewa an ɗauke mutanen zuwa wani wuri da ba sani ba.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan rikicin dake faruwa a yankin tafkin Chadi an ceto ma’aikatan agajin ne a yayin musayar wuta da aka yi tsakanin sojoji da mayakan ISWAP a wajejen garin Banki dake karamar hukumar Bama.
Zagazola ya ce a yayin musayar wutar ma’aikatan agajin sun diro daga motar yan ta’addar inda suka yi gaggawar bayyana kansu ga sojojin.
Jami’an tsaron biyu da kuma ɗaya daga cikin ma’aikatan agajin sun tsere cikin daji kuma kawo yanzu ba a gansu ba.