Sojoji Sun Ceto Lydia Simon Ɗaya Daga Cikin Ƴan Matan Chibok

Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok da mayaƙan Boko Haram suka sace a shekarar 2014.

Rahotanni sun bayyana cewa an ceto Lydia ne tare da ƴaƴanta guda uku a ƙaramar hukumar Ngoza ta jihar Borno.

A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro an yankin tafkin Chadi, Lydia na daga cikin matan da suka tsere daga sansanin ɗan ta’addar nan Ali Ngulde dake tsaunukan Mandara inda ake tsare da ita na tsawon shekaru.

Ta miƙa kanta ga dakarun sojan bataliya ta 82 dake Ngoshe a ƙaramar hukumar Gwoza  yarinyar da aka ceto tana ɗauke da ciki ɗan wata biyar kuma tayi iƙirarin cewa ta fito ne daga garin Pemi dake Chibok.

More News

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta ɗaure mutumin sa ya yi sama-da-faɗi da kuɗin marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...

NFF ta naɗa Finidi George a matsayin sabon kocin Super Eagle

An naɗa Finidi George a matsayin sabon mai horar da kungiyar ƙwallon ƙafar Najeriya wato Super Eagle. Hukumar ƙwallon Ƙafa ta Najeriya, NFF ita ta...

Gwamnan Edo Zai Fara Biyan 70,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ga ma'aikatan jihar inda za a riƙa biyan naira dubu 70,000. Gwamnan...