Shugaban NUC, AA Rasheed, ya yi murabus

Farfesa Abubakar Rasheed, babban sakataren hukumar kula da jami’o’in kasar, ya sanar da murabus dinsa daga ofis a ranar Litinin.

Rasheed ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ya yi da manema labarai, inda ya ce zai koma Jami’ar Bayero da ke Kano domin ci gaba da aiki a matsayin malami.

An nada AA Rasheed a matsayin shugaban hukumar kula da jami’o’in karkashin Honarabul Adamu Adamu kimanin shekaru bakwai da suka gabata.

Hukumar ta amince da mafi yawan jami’o’i masu zaman kansu yayin da ya kasance babban sakataren NUC.

More from this stream

Recomended