
Shugaban majalisar dokokin jihar Filato, Moses Thomas Sule ya sauka daga mukaminsa na kakakin majalisar.
Mataimakin kakakin majalisar,Gwottaon Fom shima ya sauka daga kan mukaminsa.
Mamba mai wakiltar mazabar Pankshin North, Gabriel Dawang shi ne aka zaɓa a matsayin sabon shugaban majalisar.
Hon Timothy Dantong dake wakiltar mazabar Riyom shi aka zaɓa a matsayin mataimakin shugaban majalisar.
Wasu masana na ganin wannan sauyin da aka samu baya rasa na da soke zaɓukan wasu yan majalisar da kuma zaɓen gwamnan jihar da kotun sauraren kararrakin zabe tayi.