
Shugaban majalisar dokokin jihar Edo, Frank Okiye ya kamu da cutar Coronavirus.
Mataimakin gwamnan jihar,Philip Shaibu shi ne ya sanar da haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a babban birnin jihar ranar Laraba.
Ya ce tun da farko kakakin majalisar shi ne mutumin da gwamnatin jihar take nufi ya kamu da cutar a sanarwar da ta fitar na samun bullar cutar a jihar.
Tun lokacin da ya dawo daga kasar Birtaniya, shugaban majalisar ya killace kansa.