Shin ko barin WhatsApp zai iya kare ka daga kutse?

Whatsapp daya ne daga cikin manya-manyan manhajojin sada zumunta na zamani a duniya

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

(BBC Hausa)

Bayan da WhatsApp ya tabbatar da an yi amfani da shi wajen sauke wata manhaja da za a iya amfani da ita wajen yin kutse a wayoyin salula wasu da dama sun fara tunanin daina amfani da WhatsApp.

A kasashe da dama ciki har da Indiya, mutane sun ta bayyana damuwarsu bayan da kamfanin na Whatsapp ya tabbatar cewa wasu daga cikin masu amfani da shi an yi masu kutse ta hanyar amfani da wata manhaja.

Wasu al’ummar Indian sun zargin gwamnati da hannu a kutsen ganin cewa kamfanin da ake zargin ya kirkiri manhajar mai suna NSO Group, wasu rahotannin da ba a tabbatar ba na cewa suna da alakar kasuwanci da gwamnati.

Yanzu haka kamfanin na Whatsapp ya maka kamfanin a kotu bisa zarge-zargen da ya yi masa, zarge-zargen da kamfanin na NSO ya musanta.

Ita ma gwamnatin ta India ta karyata zarge-zargen cewa tana da hannu a al’amarin.

Wannan al’amari dai ya sa wasu daga cikin masu amfani da Whatsapp sun fara sauya tunani.

Wasunsu sun fara tunanin yin watsi da shi su koma ga wasu irinsa kamar Signal da Telegram da ke suke ganin suna da kariya daga masu kutse.

Sai dai kwararru na cewa kamfanin WhatsApp din yana fuskantar kalubale da ba za a iya cewa laifinsa ba ne.

Kusan mutum miliyan daya da rabi ne ke amfani da WhatsApp a kasashe 180, sannan a Indiya kadai akwai mutum miliyan dari hudu da suke amfani da kafar sadarwar.

A cewar wani kwararren lauya, Vinay Kesari, gibin da aka samu a WhatsApp ne ya bayar da damar yin kutsen.

Shi ma wani mai rubuce-rubuce kan fasaha, Prasanto K Roy ya ce “idan har akwai manhajar da za a iya kutse a wayarka, to komai na cikin wayar tun daga abin da ake karantawa da na’urar daukar hoto ma na cikin hatsari”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

WhatsApp ya samu karbuwa a Indiya

WhatsApp ya sha ikirarincewa yana da kariya daga masu leken asiri saboda sakwannin da mutane ke aikewa junansu ne kadai suka san me sakwannin suka kunsa.

Amma masana na ganin “idan har wata manhajar kutse tana kan wayar mutum, to masu kutse suna iya ganin komai da ke kan wayar kamar yadda mai wayar yake iya gani.”

Mafi yawan masu amfani da Whatsapp sun mayar da hankalinsu ne kan barin Whatsapp din su koma wasu kafofin irinsa kamar Signal wanda ke bai wa mai amfani da su damar yin sauye-sauye.

Sai dai kuma Mista Kerasi yana ganin wannan ba yana nufin cewa manhajar ta Signal tana da kariya daga fadawa hannun masu kutse ba ne.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Indiya na daya daga cikin kasashen da suka rungumi tsarin intanet a fadin duniya

Mista Roy ya bayyana cewa “ga wadanda aka samu yi wa wayoyinsu kutse, bayanansu na wayar na cikin hatsaari inda ya kara da cewa a yanzu dai, babu wani dalili da zai hana mutum yadda cewa manhajar WhatsApp na da kariyaidan aka kwatanta da sauran kafafofin sadarwar kamarsa.

Related Articles