Shehin Musulunci ya nemi masu kuɗi da su raba wa talakawa naman Salla

Mataimakin Babban Limamin Masallacin Yobe da Cibiyar Musulunci, Malam Mohammad Ali Goni Kamsulum, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su rika raba nama don taimakawa marasa galihu a jihar, musamman a wannan lokaci da tsadar rayuwa ta yi yawa.

Mallam Kamsulum ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake gabatar da hudubarsa a ranar Lahadin da ta gabata yayin Sallar Eid-el-Kabir ta bana a cibiyar Musulunci ta Damaturu.

Mal Ali Goni ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da su so junansu kuma su kasance masu kishin ‘yan’uwansu.

Malamin addinin Musuluncin ya kuma shawarci al’ummar Musulmi da su yi koyi da rayuwar Manzon Allah SAW ta hanyar zaman lafiya da juna da raba nama ga sauran jama’a.

More News

Ƴan ta’adda sama da 260 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro

Yayin da dakarun Operation Lake Sanity 2 ke kara kai hare-hare, rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) ta yi nasarar karɓar...

Ƴan majalisar wakilai sun rage albashinsu da kaso 50

Mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun amince su rage albashinsu da kaso 50  na tsawon watanni 6 a matsayin nasu sadaukarwar da kuma nuna...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

An kama ɗan sanda kan zargin aikata fashi da makami

Wani jami'in ɗan sanda mai suna Aminu Muhammad dake aiki da rundunar ƴan sandan jihar Kogi ya faɗa komar abokan aikinsa ƴan sanda kan...