Saudiyya ta sassauto ta gayyaci Qatar taro a Makkah | BBC Hausa

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani

Hakkin mallakar hoto
Fethi Belaid/ Pool photo via AP

Image caption

Ana sa ran Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani zai kasance tare da sauran shugabannin Larabawa domin tattauna halin dar-dar da ake ciki a yankinsu

Shekaru biyu da suka wuce Saudi Arabia da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Bahrain suka sanya wa Qatar takunkumin tattalin arziki da na diflomasiyya, kan zargin cewa tana da hannu wajen daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Haka kuma kasashen sun zargi Qatar din da kusanci sosai da Iran, wadda kasashen ba sa ga-maciji da ita saboda daukar da suke yi mata a matsayin ‘yar ta’adda.

Dangantaka ta yi tsami matuka, da har lamarin ya kai Saudiyya ta haramta wa jiragen sama na kasar Qatar, bi ta sararin samaniyarta.

To yanzu dai da wannan mataki na mika goron-gayya na halartar taron shugabannin Larabawan, a kasar ta Saudiyya, alamu na nuna cewa kila za a kai ga sasantawa a tsakanin makwabtan biyu.

Sasantawar ba ma za ta tsaya tsakanin kasashen biyu ba kadai har ma da sauran kasashen da suka mara wa Saudiyyar baya wajen mayar da Qatar din saniyar-ware.

Wannan gayyata dai ta samu ne bayan da tun da farko Qatar din ta yi korafin cewa, ba a gayyace ta ba wajen halartar taron-kolin, wanda za a tattauna batun kai hare-hare kan kayayyakin aikin mai da tankokin dakon man.

Bayan wannan korafi ne sai kuma Qatar din ta biyo baya da sanarwar cewa an aika mata goron-gayyatar halartar taron wanda shugabannin kasashen Larabawan za su yi a Makkah, ranar Alhamis.

Sai dai kuma zuwa yanzu hukumomin kasar ta Qatar ba su sanar cewa ko za su halarci taron ba ko kuma ba za su je ba.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa É—aya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faÉ—a tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...