Saudiyya ta kama ‘yan gidan sarauta uku

Crown Prince Mohammed bin Salman

Ana kallon Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a matsayin wanda shi ne ainihin ke mulki a Saudiyya

Wasu manyan ‘yan gidan sarautar Saudiyya uku sun shiga hannun hukumomin kasar, cikinsu har da kanin Sarkin kasar Salman.

Ba a bayyana dalilan kama su ba, amma wasu jaridun Amurka na cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salma ne ya bayar da umarnin daukar wannan matakin a kansu.

Biyu daga cikin yarimomin na da karfin fada a ji a daular ta Saudiyya.

A 2017 Yarima Mohammaed bin Salman ya taba bayar da umarnin a kama kuma a tsare wasu manyan attajirai da ministocin kasar da kuma wasu manyan ‘yan gidan sarautar Saudiyyar a wani otel mai suna Ritz-Carlton da ke Riyadh.

Ana kallon Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a matsayin wanda shi ne ainihin ke mulki a Saudiyya, tun bayan da mahaifinsa ya nada shi yarima mai jiran gado a 2016.

‘Yan gidan sarautar uku sun shiga hannun jami’an tsaro ne tun safiyar jiya Jumma’a, kamar yadda jaridun New York Times da Wall Street Journal suka wallafa.

Sunayen wadanda ake tsare da su: Ahmed bin Abdulaziz – wanda kanin Sarki Salman ne, da tsohon yarima mai jiran gado Mohammed bin Nayef, da kuma dan uwansu Yarima Nawaf bin Nayef.

Mohammed bin Nayef ya taba rike mukamin ministan cikin gida kafin aka cire shi daga mukamin bayan da Yarima Mohammed bin Salman ya sa aka yi masa daurin talala a 2017.

More News

Sojoji Sun Ceto Mutane Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Filato

Dakarun rundunar Operation Safe Haven dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Filato da wani É“angare na jihar Kaduna sun samu nasarar ceto mutane...

Matatar Mai Ta Kaduna Za Ta Fara Aiki A Ƙarshen 2024

Kamfanin Kaduna Refining and Petrochemical Company KPRC ya ce matatar mansa za ta fara aiki a shekarar 2024. Mustapha Sugungun managan matatar man ta KRPC...

Manyan dillalan mai za su fitar da litar man fetur miliyan 300 a wannan makon

Ƙungiyar MEMAN ta manyan dillalan man fetur da dangoginsa ta ce mambobinta sun fara lodin mai har lita miliyan 300 a cikin makon nan...

Kotu ta É—aure mutumin sa ya yi sama-da-faÉ—i da kuÉ—in marayu

Babbar kotu a jihar Borno ta yanke wa Isiyaku Ibrahim hukuncin shekara ɗaya a gidan yari da zaɓin biyan tarar naira dubu 100 saboda...