
Kasar Saudiya ta sanar da zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane biyar yan kasar hudu da kuma wani dan kasar Masar bayan da aka same su da laifin kai wani mummunan hari a wurin ibada.
Kamfanin dillancin labarai na Saudiya ya bayyana cewa an kai harin ne a yankin Al-Ahsa inda mutane biyar suka mutu wasu kuma da dama suka jikkata.
Kafafen yada labarai na kasar da suka bada rahoton ba su bayyana lokacin da abun ya faru ba ko kuma wurin ibadar da aka kai harin.
Dan kasar Masar din shi ne aka samu da laifin harbin jami’an tsaro tare da yunkurin tayar da bom sai kuma aikata laifin shiga kungiyar yan ta’adda.
Ana zargin mutane uku da taimaka masa wajen shiryawa da tsara harin.
Mutum na hudu an same shi da laifin kin sanar da hukuma kan shirin kai harin da kuma laifin zuga wasu su shiga kungiyar ta’addanci.