Sarki Salman na Saudiyya ya kori ‘yan gidan sarautar daga muƙamansu

Crown Prince Mohammed bin Salman

Bayanan hoto,
Ana yi wa Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman kallon shugaban Saudiyya

An kori jami’an kasar Saudiyya da dama, ciki har da iyalan gidan sarauta guda biyu.

Wata sanarwa ta bayyana cewa Sarki Salman ya sauke Yarima Fahad bin Turki daga kan mukaminsa na kwamandan hadakar dakarun tsaron kasar da ke jagorantar yakin da ake yi a Yemen.

Kazalika an sauke dansa, Abdulaziz bin Fahad, daga mukamin mataimakin gwamna.

Mutanen biyu, tare da karin mutum hudu, suna fuskantar bincike bisa “zargin wadaƙa da kudi” a Ma’aikatar Tsaron kasar.

Yarima Mai Jiran Gadon Sarautar Saudiyya Mohammed bin Salman, wanda shi ne dan sarkin kuma ake yi masa kallo a matsayin mutumin da zai gaji Sarki Salman, yana jagorantar yaki da cin hanci da ake zargin ana aikatawa a gwamnati.

Sai dai masu suka na cewa yana yin hakan ne da zummar kawar da mutanen da ka iya yi masa zagon-kasa a yunkurinsa na zama sarki.

A farkon wannan shekarar, mujallar Wall Street Journal ta ruwaito cewa an kama manyan shugabannin gidan sarautar kasar guda uku, cikinsu har da kanin sarkin, Yarima Ahmed bin Abdulaziz da kuma tsohon Yarima mai jiran gado Mohammed bin Nayef.

Babban abin da ya ja hankalin duniya kan yaki da cin hanci a Saudiyya shi ne kamen da aka yi wa wasu fitattun ‘yan gidan sarautar kasar, ciki har da ministoci da ‘yan kasuwa, inda aka tsare su a shahararren otal din nan na Ritz-Carlton da ke Riyadh a 2017.

An saki galibinsu daga bisani, kodayake sai da suka bayar da dala biliyan 106.7.

Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman mai shekara 35, ya sha yabo daga kasashen duniya a 2016 lokacin da ya yi alkawarin kawo sauye-sauye a fannin tattalin arziki da zamantakewa a kasar da ke da wuyar sha’ani.

Sai dai ya rika shan suka kan batutuwa da dama, ciki har da kisan dan jaridar Saudiyya Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin kasar da ke Istanbul na Turkiyya.

More News

Tayoyin jirgin saman Max Air sun fashe a Yola

Jirgin saman kamfanin Max Air ƙirar Boeing 737 mai rijistar namba 5N-ADB dake ɗauke da fasinjoji 118 da ma'aikata 6 ya gamu da matsala...

Ɗan majalisar wakilai ta tarayya ya mutu

Hon. Olaide Akinremi Jagaba mamba a majalisar wakilai ta Najeriya dake wakiltar mazaɓar Ibadan North a majalisar ya mutu. Kawo yanzu babu cikakken bayani kan...

Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure

Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan wata doka za ta tilastawa masu yin aure yin wasu gwaje-gwajen lafiya gabanin...

An kashe kwamandan soji a Katsina

An kashe kwamandan sojoji na wani sansanin soji da ke Sabon Garin Dan’Ali a karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina a wani harin kwantan...