Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Muhammad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su fara duban watan Ramadan ranar Lahadi.
Sarkin Musulmin ya sanar da haka ne cikin wata sanarwa da, Salisu Shehu sakataren majalisar koli ta addinin Muslunci ta ƙasa ya fitar.
Sanarwar ta ce za a fara azumin Ramadan kai tsaye ranar Talata matukar ba a ga watan ba a ranar Lahadi.
Kwamitin ganin wata na ƙasa shi ne ya bayar da shawarar fara duban watan a ranar Lahadi wacce tayi dai-dai da 29 ga watan Sha’aban shekarar 1445 bayan hijira.
Sarkin Musulmin ya roƙi Musulmi masu hannu da shuni dake ƙasarnan da su bada sadaka ga mutanen da basu da ƙarfi da suke maƙotaka da su a lokacin azumin dama bayan azumi.