Sace-sacen motoci ya yawaita a Adamawa—Ƴan sanda

Ana ci gaba da samun karuwar sace-sacen motoci a jihar Adamawa, kamar yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar.

Rundunar ‘yan sandan ta bayyana haka ne a wata sanarwa a safiyar ranar Asabar, tana mai sanar da jama’a kan karuwar satar motoci, musamman a kananan hukumomin Yola ta Arewa da Yola ta Kudu da kuma Girei.

Sanarwar ta fito ne daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Suleiman Nguroje.

Ya ce a wani mataki na dakile tashe-tashen hankulan, rundunar za ta fara gudanar da bincike mai zurfi a yankunan da lamarin ya shafa wanda ka iya janyo cunkoson motoci.

“Saboda haka kwamishinan ‘yan sanda ya yi kira ga masu ababen hawa da su fahimce su domin matakin na kare lafiyarsu da tsaron lafiyarsu ne,” in ji Nguroje.

Ya yi kira ga jama’a da cewa za su iya kiran  rundunar ‘yan sanda a wadannan lambobin 08089671313, idan wani lamari ya faru.

More News

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Majalisar dokokin Zamfara ta tsige kakakinta saboda tsanantar rashin tsaro a jihar

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, tare da nada Bashar Gummi, a matsayin kakakin majalisar. Hakan ya biyo bayan kudirin da dan...

Ƴan bindiga sun kashe mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane shida da wasu ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari a jihar. Jami’in hulda...

Majalisa ta gayyaci jagororin hukumomin tsaro saboda tashe-tashen hankulan da ake fama da su

A ranar Laraba ne majalisar wakilai ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu...