Majalisa ta gayyaci jagororin hukumomin tsaro saboda tashe-tashen hankulan da ake fama da su

A ranar Laraba ne majalisar wakilai ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da kuma manyan hafsoshin tsaro kan tabarbarewar tsaro a babban birnin tarayya Abuja.

Kudurin majalisar dai ya biyo bayan amincewa da kudirin da dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Aguta ta jihar Anambra, Mista Dominic Okafor ya gabatar.

Dan majalisar, a yayin da yake jagorantar muhawarar ya bayyana cewa, kar fa a manta babban birnin tarayya Abuja shi ne fadarmr gwamnatin tarayya daga inda ake samar da ƙudurori na kasa, inda ya kara da cewa hedkwatar gwamnatin tarayya da ma hukumomin kasa da kasa na cikin birnin mulkin kasa.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar Nasarawa dake kusa da jihar ta sanar da shirin sanya na’urorin tsaro a fadin jihar domin dakile matsalolin tsaro da ake fama da su a jihar wanda ya kamata a kwaikwaya a Abuja kasancewar cibiyar al’umma ce kuma ya kamata ta kasance wuri mafi aminci a cikin kasar.”

Majalisar ta shawarci ministan birnin tarayya Abuja Nyeson Wike da ya dala kyamarori ta ko’ina domin maganin matsalar tsaro.

More News

Mutane da dama sun mutu bayan motar fasinja ta taka bam a Borno

Akalla mutane 16 ne ake fargabar sun mutu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wata motar fasinja da ke kan titin Baga-Kukawa a...

Wasu É—aliban Jami’ar Jihar Nasarawa sun mutu a lokacin turmutsutsin karÉ“ar tallafin abinci

Dalibai biyu daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK) sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya barke a lokacin da suke kokarin...

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...