Rundunar yan sanda ta tabbatar kisan ƴan sanda 4 a harin da aka kai wasu bankuna a Benue

Babban Sifetan Yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya tura karin jami’an yan sanda zuwa jihar Benue biyo bayan harin da aka kai kan wasu bankunan kasuwanci daban-daban guda hudu a jihar.

A ranar Juma’a wasu yan bindiga suka kai farmaki garin Otukpo dake jihar inda suka shafe sama da awanni biyu suna fashi a bankunan huɗu.

Andrew Aganga wani mazaunin garin ya ce yan fashin sun kuma kai hari kan ofishin yan sanda dake kusa da bankunan.

Da yake tabbatar da faruwar haka mai magana da yawun rundunar yan sandan Najeriya, Olamuyiwa Adejobi ya tabbatar da cewa John Adikwu baturen yan sanda na Otukpo da karin wasu yan sanda uku sai kuma farar hula uku na daga cikin waɗanda aka kashe a harin.

Ya ƙara da cewa an kashe biyu daga cikin ƴan bindigar.

Adejobi ya ce babban sifetan yan sandan ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka kai harin.

More News

Najeriya za ta dena shigo da man fetur a cikin watan Yuni – Dangote

Aliko Dangote mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka ya ce Najeriya za ta daina shigo da man fetur a cikin watan...

An ceto mutane 9 daga wani ginin bene da ya ruguzo a jihar Niger

Mutane 9 aka samu nasarar cetowa daga wani ginin bene mai hawa ɗaya da ya ruguzo a yankin Sabon Gwari dake garin Minna babban...

An yi faɗa tsakanin masu sayar da waya da sojoji a kasuwar Abuja

Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tura jami’an leken asiri zuwa kasuwar Banex – wata kasuwar kayan lantarki da na’urorin sadarwa da ke...

Yawan Mutanen Da Suka Mutu A Wutar Da Wani Matashi Ya Cinnawa Wani Masallaci A Kano Sun  Karu Zuwa 16

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon wutar da wani ya cinnawa wani masallaci a ƙauyen Gadan a...